Dan takarar shugaban kasa na jam,iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada sakonsa na dawo da cigaban tattalin arzikin yan Najeriya a tarukan yakin neman zabe da aka gudanar a jahohin Anambra da Cross Rivers.
Yayinda yake jawabi a Akwa da Calabar many an biranen Anambra da Cross Rivers Tinubu yace zai bada muhimmacin GA samarda ayukkan yi ga dinbin matasa yan Najeriya da basuda aikin inda hakan ne kawai zai habbaka tattalin arzikin kasar.
A filin wasan Calabar Tinubu yayi godiya ga mutanen garin dama gwamna Ben Ayade dangane da tarba ta musamman da suka yi masa
" nayi matukar godiya. Allah ya albarkaceku ya albarkaci zuri,arku ya kareku da iyalanku daga sharrin makiyanku. Allah ya kuma tabbbatarda far in ciki a gareku. Yayanku zasu zamo abun alfahari kuma su fiku daukaka. Tun safe kuna nan kuna jiran kuji me zamu zo mu fada maku.
Yayinda yake tuna masu da mulkinsa a jahar Lagos Tinubu yayi alkawarin habbaka tattalin arzikin Najeriya.
" idan muka tuna mun taba yin alkawalin habbaka jahar Lagos. Mun gina hajar Lagos mun kuma habbaka tattalin arzikin jahar. Kuna bukatar ci gaba? To mun kawo maku tallar jam,iyyar mu. Ina mika godiya ta mussamman ga John Enoh da irin ban girman da kayi mana haka ma madam Mary Ekpere. Allah ya albarkaceku bazakuyi nadamar goyon bayanku a garemu ba. Nayi muku alkawarin ci gaba mai dorewa ta hanyar samarda ayukanyi. Munyi alkakawalin habbaka hanyoyin sufurin ruwa Wanda Calabar sai tafi Miami dake jahar Florida a Amerika. Za,a samu kudaden shiga zakuci moriyar hakan in sha Allah Calabar saita zamo cibiyar yan yawon bude ido.
Akan Dan takarar jamiyyar PDP kuwa Tinubu yace Atiku ba abun yarda bane zai sayarwa kansa da Najeriya.
"Karku manta da karairayin PDP na shekaru 16, amma sun kasa bada wutarda zata gasa masara. Sai karyar tsiya. Yunkurinsu na sayarda kayyakin al,umma bazai haifawa Najeriya da mai ido ba domin kuwa kawunansu zasu sayarwa kadarorin mu.
A taron na Calabar gwamna Ben Ayade yace mutane sun taru ne domin taya murnan cin zabenda za,a gudanar 25 ga February. Ya kuma gayawa dan takarar cewa abunda mutanensa ke bukata shine a habbaka tashar jirgin ruwa ta Bakkasi sai kuma babban titin mota da zai hada kudanci da arewacin kasar nan. Gwamnan yayi alkawalin cewa zasu zabi Tinubu kwai da kwarkwata basai ya fito kamfe ba.
Manyan jam,iyyar APC da suka halacci taron sun hada da Dr. Betta Edu, shugaban mata ta kasa, Alphonsus Eba dan takarar gwamna, Prince Bassey Otu da tsohon shugaban majalisa Senator Udoma Egba. Inda dukansu suka jaddada goyon bayansu ga Tinubu da mataumakinsa.
A dayan hannun kuma a taron kamfe na Anambra Tinubu yayi kira ga mutanen Anambra da cewa su zabi mutumenda suka San zai kare muradinsu ya kuma yi kira garesu dasu guji yan takara masu yada kabilanci.
Yace dukda cewa dan takarar jamiyar labor party dan jahar Anambra be amma mutanen jahar zasuyiwa Kansu zabi duba da irin yadda ya kasa kawo wani muhimmin ci gaba a jahar da sune tattalin kudin daya boye a asusun bankuna.
Tinubu yace Obi na tinkaho da zai samu kuri,un yan jahar ta Anambra ne saboda shi dan jahar ne amma shi Tinubu mulkinsa a matsayin gwamnan jahar Lagos ne zai masa kamfe, inda ya nunawa yan Najeriya cewa shi mutum ne maras kabilanci dake maraba da kowa da kowa daga kowane bangare na Najeriya.
Yace kuyi Allah wadai da duhun kabilanci da tsana. Ku guji mutannenda ke ganin cewa su sun fiku saboda sun samu damar sace kudaden Al, umma Wanda suke gani hakinsu ne suda iyalansu bawai su habbaka rayuwarku ba.
"Wannan zaben ba zaben nuna kai bane ba kuma taron big brother Nigeria bane. Wannan zaben ana zancen wazai iya gina Najeriya ya habbaka kasa tareda kawo hadin kan yan kasa a matsayin yan uwa.
"Nasan akwai wasu mutanenda bazasu zabeni ba wudanda basa sha,awar irin ci gaba da zamu kawowa kasa, amma dukda haka ni ina kaunarsu saboda yan Najeriya ne kuma zanyi kokarin in rikesu a matsayin nawa saboda dukda cewa sun kini".
Da ace ban riki duk dan Najeriya a matsayin dan uwa ba da bazan dauki dan uwanku Ben Akabueze a matsayin kwamishinan kasafin kudin ba a lokacinda nake gwamnan Lagos. Yanzu haka yana iya kokarinsa a matsayinsa na darekto ofishin kasafin kudi na kasa.
Bana tsanar mutum saboda yarensa, kabilarsa ko addininsa. Allah bai amince mana da mu zamo masu nuna wariya da kabilanci ba. Nayi kira gareku kada Ku zamo masu tsanar mutum saboda sunanshi ko sashenda ya fito kuso nuna cikin amana da adalci.
dan takarar yayi alkawalin samarda ayyuka ga dinbin matasan da basuda aikinyi da kuma yakar talauci tabbatarda yalwa.
" tsare tsare na sun kunshi samarda cibiyoyin kamfanoni da zasu koyarda sanaoi na zamani, su kuma kera kayan masarufi da zasu habbaka tattalin arzikin Najeriya".
"Samarda masana,antu da zasu ringa sarrafa kayan masarufi a nan Awka da ma wasu sassa na kudu masu gabaccin Najeriya zasu habbaka tattalin arzikinku. Zai rage talauci zai kuma samarda hanyoyin dogaro dakai."
"Gwamnatina zata kirkiro cibiyoyin habbaka ayukan noma da kuma samarda ayuka na gari da dogaro da kai ga yan kasa".
Ya kuma yi alkawalin farfado da fannin ilimi yayinda kuma yake magana akan nasarorinda ya samu a jahar Lagos dan takarar yana cewa " nasan zan iyayi wudannan abubuwan saboda nayi makamancin hakan a jahar Lagos Wanda yasa daya daga cikin yan Adawata dake daga jaharku baya iya zama cikin Ku yana zaune a Lagos. "
" Ina zaune a Lagos saboda ina alfahari da ci gaban da na Samar a jahar, amma abokin takara ta baya iya zama cikin Ku saboda ya san bai maku abunda ya dace ba."
"wannan marowacin yaki yayi amfani da kudin al, umma wajen habbaka rayuwarsu amma yaje yasa kudi a asusu ya boye. Meye amfanin kudi a asusu kaki ta taimakawa mutanenka a lokacinda suke bukata?"
"Irin wannan mutum hatsarine a shugabanci kada Ku sake ya zamo shugaban kasarku."
Sabanin irinsu kara Ku zabi shugaban da keda burin kawo ci gaba mai dorewa a kasa.
Ofishin yada labarai na Tinubu
Tunde Rahman
January 31, 2023
Tags
Hausa