Shin Wa Emefile Yake Yiwa Aiki?


Lokaci yayi da ya kamata mu ringa amfani da mahanga ta basira wajen fahimta da kuma la,akari da inda duniya ta maida gaba. Sannan kuma dole mu jama,ar Arewa muyiwa kanmu kiyamul laili wajen ilmantarda dinbin jama,ar mu da ta zamo barazana ga sauran sassan kasar nan. 

Satinda ya gabata wani masani kuma marubuci  mai suna Moses Oludele Idowu yayi wani rubutu a Jaridar Abuja Network News inda yayi wannan tambayar " Wa Emefile yake yiwa aiki". 

Marubucin yayi tambayoyi muhimmai wanda daga karshe dai ya yanke shawarar cewa ga dukkan alamu Emefile karen farautar Turawan yamma ne, kuma su yake yiwa aiki da zimmar cimma burinsu na samun abunda suke kira cashless economy.

Cashless economy wani tsari wanda turawan yamma suka kirkiro da zimmar daina hudda da takardun kudi, duk kudade zasu koma bankuna. Cinikayya da saura mu,a mala ta kudi zata koma ta hanyar amfani da transfer, cheque, da dai saura hanyoyin juya kudi a karkashin bankuna. 

A cewar su wannan zai rage yawan ta,adi da ta,asarda ake amfani da takardun kudin wajen aikatawa kamar cinikayyar haramtattun makamai, miyagun kwayoyi, biyan kudin fansa da sauransu. A nasu ganin kuma zai kawar da matsalolin fashi da makami da kuma yawan asarar da ake tafkawa sakamakon gobara da sauransu. 

Amma masu ilimi na ganin cewa wannan wata hanya ce ta zata mallakawa gwamnatoci rayuwar bil Adam gaba dayanta, dan Adam zai rasa yancin gaba daya. 

Domin yanzu lokacinda ake amfani da takardun kudi mutum zai iya shiga shago ya sayi abunda yakeso babu Wanda yasan me ya saya ko na nawa ya saya. Amma da zarar komai ya koma hanyar transfer to gwamnati ta samu hanyar sa ido ga duk wani abu daya shafi rayuwar dan Adam, sun san me ka saya, a wane gari kayi amfani da katin ka, suna da cikakken bayani na duk yadda kake gudanarda rayuwarka da zarar kayi wani abu da ya sabawa tsarinda sukeson su doraka a kanshi za,a iya kulle account dinka koma a goge kudinda ke ciki. Nan take a tsiyata ka.

Haka masannan suna ganin idan wannan tsarin ya kankama to mutum bashida wani inci na sukar lamirin gwamnati ko kuma saba masu domin gwamnatin nada damar kulle asusun ajiyarka Wanda dole sai kayi abunda akeso. 

Misali shekara biyu da suka gabata da gwamnatoci suka kawo tsarin allurar riga kafin cutar corona mutane da dama a fadin duniya basu aminta da wannan tsarin ba kuma sunki aminta da ayi musu allurar. Wanda hakan ya janyo gwamnatoci suka saka dokar hana mutane zirga zirga daga kasa zuwa kasa, ko daukar aiki ko bada kwqngila da sauransu har sai mutum ya nuna wannan shaidar. Daga karshe dai dubun dubatar mutane ko ince daruruwan milyoyin mutane sun kauracewa wannan rigakafin kuma daga baya saiga bayanan sirri na tabbatarda cewa kodai riga kafin na dauke da wasu cutuka na dabban ko kuma baya amfaninda aka ce yanayi na kare mutum kamuwa da cutar ta corona.

Amma da ace wannan tsarin na cashless policy ya kankama to gwamnati kawai zata kulle account din wani Wanda baiyi rigakafin ba ba don Allah ba ma dole mutum yaje yayi saidai daga baya a taru ana nuna wa juna yatsa tsakanin gwamnati da yan kasa.

Mu dawo kan zan Emefile da ko wa yake yiwa aiki. Sannin kowa cewa a duk lokacinda bature ya kirkiri wani sabon tsari, ko magani ko ya kirkiri wata sabuwar na,ura da yake ganin zata iya zuwa da wata illa ko cuta ga alumma to baya gwajin wannan na,urar ko tsarin a kasashensa saboda gudun kota komo. 

Abunda sukeyi saisu hada kai da rubabbin yan siyasar Africa a basu kwangila mai tsoka su kuwa sai dauko wannan tsarin ko na,urar su kawo kasashesu na gado azo a gwada idan tayi ruwa rijiya idan kuma batayi ba masai.

Lokuta da yawa an samu irin wudannan misalai kamar yadda aka samu matsala da kamfanin Pfizer a kano shekaru ashirin da suka gabata inda suka kirkiri wani magani da ya kamata a gwada a jikin zomaye ko zabi amma da yake ana bukatar samun sakamakon gaggawa sai aka kawoshi kano aka gwada akan jinjirai da kananan yara. Daga karshe wannan riga kafin yayi sanadiyyar mutuwar dubun dubatan jarirai Wanda daga karshe sai da kamfanin na Pfizer ya dauki alhaki ya kuma biya diyya.

Irin haka ta faru baso daya baso biyu ba, don haka shekarar da ta gabada da kamfanin modana ya kirkiri riga kafin cutar corona ya kuma yi yunkurin jaraba tasirinta a kan turawa nan take suka ringa tada kayar baya ai suna fitowa kafafen yada labarai suna Allah wadai da kamfanin suna kuma kira kamfanin da suje Africa su gwada maganinsu a can ake gwaje gwajen magunguna ba a cikinsu wayayyin mutane ba. 

Wannan shiya kawo mu kan Emefile da kuma su wa yake yiwa aiki. Emefile ya zamo dan anshin shatan turawan yamma. Kuma wannan tsarin na sauya kudi anyishi ne da zimmar rage takardun kudinda ke hannun yan Najeriya ne domin a yi bincike a ga illolin da tsarin zai haifar a kuma nemo masu magani. A takaice dai mun zamo wani zomo ko akuya da ake gwada wannan tsarin akai a gani idan tayi ruwa rijiya idan batayi ba Masai. 

A wannan gabar mutum zai iya tambayar shin to shi shugaba Muhammadu Buhari zaman me yake? Shin yanada masaniya akan wannan tsarin? Kuma me yasa ya bada kai bori ya hau? Wannan zance ne na wani lokaci kuma zanuyishi idan da rai da lafiya.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post