A rana mai kamar ta yau ne 15 January 1966 wato shekaru 57 da suka gabata ne wasu yan kabilar Igbo masu yunkurin juyin mulki a karkashin Jagorancin Chukwuma Kaduna suka hallaka firaministan Najeriya Sir Tafawa Balewa da kuma firimiya na yankin Arewa wato Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da sauran manya siyasar arewacin Najeriya inda suka dora General Aguinyi Ironsi akan mulki bayan haka.
Tarihi ya nuna tsantsar cin amana irin ta inyamuri kamar yadda Sir Ahmadu Bello ya dauki Major Nzegu a matsayin danshi, yayi mashi komai a rayuwa ya kuma taimaka mashi wajen karo ilimi da samun Karin girma a aikin shi na soja amma daga karshe Nzegu yayi amfani da wannan damar wajen Hallaka Sardauna da mai dakinsa wacce ta daukeshi kamar uwa da kuma sauran abokan aikinsa makusanta kuma shakikai.
A daren 14 ga watan January 1996 wasu manyan sojoji yan kabilar Igbo da tsiraru daga bangaren yarbawa sunyi bore inda suka fara kaddamarda gisan gillah akan manyan sojoji yan asalin Arewacin Najeriya abunda ya kai har ga manyan shuwagabannin siyasa.
A safiyar 15 January 1966 labari ya riga da ya zagaya birane da kauyuka na Najeriya cewa sojojijin sun kaddamarda Juyin mulki sun kuma kashe manyan sojoji da na siyasa tare da nada sabuwar gwamnati a karkashin jagorancin Gen. Ironsi.
Cikin manyan shuwagabannin siyasar Arewa da aka kashe kuwa an samu gawarwakin wasu a wannan ranar wasu kuma sai bayan kwanaki da kuma kai ruwa rana sannan aka samo gawawwakinsu.
Basai an fada ba duk inda kabi a yankin Arewa bakajin komai sai kuka da Allah waddai, inda su kuma yan kabilar inyamurai da ke zaune a wudannan bangaren na arewacin Najeriya sai murna suke a fili suna nuna jin dadinsu. Tarihi ya nuna cewa wannan shine makasudin yankin basasar kasar.
Bincike ya nuna sojojin masu juyin mulki sun wulakanta manyan Arewa kafin su kashesu, inda har suka tilastawa wasu daga cikin shuwagabannin siyasar shan giya da yin wasu abubuwa da addinin musulunci ya haramta kafin kuma daga karshe suka kasheshu.
Haka bayanan sirri sun nuna cewa bayan tilastawa Firaminista Balewa shan giya sojojin sun daureshi a bayan mota suka ringa janshi a titi har saida ya cika kafin sukaje suka wurgarda gawarsa a bayan gari. Wannan abun da makamancin yayi matukar batawa yan Arewa rai inda kuma manya da kanana sukayi alwashin daukar fansa.
Abun mamaki kuma shine duk da cewa su wudancan sojojin sun fake ne da juyin mulki suka aikata wannan mummunan aikin amma basu kashe shugaban kasa na wancan lokacin ba Wanda ya kasance dan kabilarsu ta Igbo basu kuma kashe firimiya na bangaren yarbawa ba dana inyamurai.
Wannan ne ya janyo juyin mulkin ramuwar gayya daga sojojin Arewa wudanda suka hada da General Murtala Muhammad, Gen. T.Y Danjuma, Major Joe Garba da sauransu inda suma suka hallaka Aguinyi Ironsi suka kuma dawo da mulki Arewa a hannun Gen. Gowon.
Wannan shine makasudin jerin gwanon juyin mulkin da aka shafe shekara da shekaru anayi a Najeriya Wanda ya zamo ummul haba,isin tabarbarewar tattalin arzikin kasar da kuma haddasa rashin jituwa a tsakanin bangarorin guda biyu.
Tags
Hausa