Naja,atu, Naja,atu, Naja,atu So Nawa Na Kira Sunanki.
Idan dai har a wudannan shekarun, shekara 67- za,ace ya mace na ja ya fado ja ya dauka hadi da yawon Allah baku mu samu to tabbas Sanata Bola Tinubu nada Jan wajen ganin ya tallafawa irin wudannan mutanen idan ya zamo shugaban kasa. Satinda ya wuce Naja,atu Mohammed ta sauya sheka daga bangaren Bola Tinubu zuwa Atiku Abubakar. Harda fadar cewa kodan gidajen jaridun kudancin Najeriya bai kamata abar Sanata Bola Tinubu ya zamo shugaban kasar Najeriya ba.
Naja,atun da ke nuna cewa kullum tana gefen gaskiya da adalci ku kuwa take nuna hakan, ace wai itace yanzu a tawagar Atiku Abubakar kawai domin yada manufarta ta Allah baku mu samu. Tun daga wannan ranar sai cara take tana ihu wajen batanci da qoqarin aibata Sanata Bola Tinubu a idon duniya. Harda fadar cewa tan takarar baya iya rike kofin shayi kamar itace mai renon Tinubu a lokacinda take wannan gefen.
Irin su Naja,atu da dan uwanta Bwala yan banza ta fadi anzo ne aci banza sai banza bata samuba don haka suka yanke shawarar a kwashe tabarmar kunya da hauka.
Da ace Naja,atu nada wayo to da ta noke ko kuma ta ware ba tareda tada kura ba da hakan zai fi mata sauki amma bawai tabi gari da kida ba tana janyowa kanta abun fadi a gari. Dukda dai ance tabarmar kunya da hauka ake nade ta kuma idan mutun ya duba ya kuma yi la,akari da cewa Najaatu Mohammed kamar Atiku Abubakar basu taba yin nasara a wani zabe da suka tsaya da Kansu ba cikin sama da shekaru talatin da suka wuce na rayuwarsu saidai kawai mutum yace Allah raka taki gona.
Najaatu Mohammed tace wai Tinubu baya iya daga kofin shayi, ta kara da cewa dan takarar na fama da ciwon dementia ga dukkan alamu dai Najaatu na magana ne dangane da wani Tinubu dabban ba Wanda muka sani ba, ba kuma Wanda muke gani yana yawo a sassa dabban dabban da jahohi dabban dabban na kasar nan wajen yakin neman zabeba. Sabanin dan takarar ta Atiku Abubakar Wanda ya makale a Chatham house ya kasa karatu a rana tsaka kuma a farar takarda. Wanda saida dan anshin shatarsa Reno Omokri ya haura kan fage ya farfado dashi. Wannan shine alamun dementia.
Bawai ina ganin laifin Najaatu bane na sauya sheka a,a irin labaran kanzon kuregenda take yadawa ne kawai saboda iya maula nake kokarin rushewa.
Tinubu yana nan daram dam yana kuma ci gaba da yakin neman zabensa ba gudu ba ja da baya, tun ranarda ya dawo daga Saudi Arabia babu wata rana data wuce ba tareda wani taro ba domin cimma wannan manufar.
Idan har gwamnonin arewa masu jini a jika dake fadi tashi wajen tallata tafiyar Tinubu kamarsu Ganduje,Elrufai,Bagudu,Badaru,Suleiman, Masari, Yahaya Bello da sauran gwamnoni arewa basuga alamun dementia a Tinubu ba tabbas Najaatu tayi gamo ne kuma ga dukkan alamu ta fara sambatu.
Tabbas a cikin ganawarsa da manyan mutane na sassa dabban dabban na kasar nan da Asiwaju Tinubu yana haduwa da duk wasu masu ruwa da tsaki a kowane fanni daya shafi Najeriya amma acce duk a cikinsu ba a samu ko mutum dayaba daya ga alamun dementia taredashi ba sai lashe money Najaatu to wannan abun dubawa ne. Kokarin batawa Tinubu suna da Najaatu keyi da zimmar gyara tukunyar miyarta bazai hana tafiya Asiwaju Bola Tinubu cimma Nasara ba saboda tafiyace waccr lokacinta yazo. Zan sake ziyartar ki Najaatu.
Prince Kassim Afegbua
Tsohon Kwamishinan Yada Labarai Edo State.
Tags
Hausa