DAGA: Comrade Nura Ahmad Muhd Mai Yadi Bichi
.
Abba Kabir Yusuf ya debo kalar jama'ar su, ya shigo da su filin jirgi, a kan hanyar sa ta zuwa Abuja.
Suna tsaka da aikata masha'ar su, sai ga tawagar mai dakin shugaban hukumar DSS na kasa ita ma ta zo filin a kan hanyar ta ta zuwa Abujan.
Babu shakka jami'an tsaron da suke kare ta su ne suka sa duka, amma ba ita ce tasa su ba.
Saboda nuna rashin tarbiya irin ta Yan KWANKWASSIYA da suka Saba yiwa masu Mutunici a idon DUNIYA.
Karya ne irin ta kamfanin Jaridar. JA,AFAR JA,AFAR suk yi mata cewa, hajiyar ce ta sa Jami'an tsaron ta su yi duka.
saboda sanin kowane wannan Kamfanin Jaridar da suka fara wallafa wannan Labari yasaba yiwa masu Mutunici Shari da kage domin biyan bukatar kansu.
Hakika a yanda yan kwankwasiyya suka cika gurin, suna yin abin da kowa yasan su da shi.
Babu wani abu da za ka zo da shi su saurare ka har su ba ka hanya ka wuce in ba duka ba ko ashar.
Dangane da batun wai hajiya A'ishan ce tasa a daki mai daukar ta hoto kuwa, sam ba haka ba ne jami'an tsaron ne suka cika aikin su.
Na tabbata shi kan sa kwankwaso in na sa jami'an tsaron sun ga wani yana daukar hoton sa ba da yardar sa ba, sai sun tumurmusa shi.
Batun da yan jarida suka yi kuwa cewa wai ta ce baza ta barshi ya zama gwamna ba, ai komai dodewar basirar mutum da jahilcin sa, ya san karya ce.
Saboda ba ita ce take bayarwa ba, ALLAH ne mai bayarwa. wannan karya aka yi mata.
Kawai yan jaridar sun fadi haka ne don su sami kudi a wajen gidadawa masu zuwa mayar da martani.
Ko shakka babu duk mai hankali zai kaddara cewa wannan mugun gamo da yan kwankwasiyya suka yi.
1) Al-hakin Sheikh Isah Aliyu Ibrahim Fantami ne, saboda cin mutuncin da suka yi masa, shima a filin jirgin Sama na MALAM AMINU KANO.
2) Al-hakin Sule Lamido ne da Dansa Mustapha Sule Lamido domin Yan KWANKWASSIYA sai da suka farfasa masu Motor sukaci mutuncin Sule Lamido Dansa harkuka sai da yayi a Filin Jirgin sama na Malam Aminu Kano.
3) Al-hakin Amb, Aminu Wali ne domin a gidan Sarkin Kano. Babu irin cin mutuncin da basuyimasa ba. a matsayinsa na dattijo.
Kai a taikaice Yan KWANKWASSIYA babu wanda suka bari idan suka tashi cin mutuncin Mai mutuncin.
Wanda har zuwa yau bamu ji kwankwaso ya fito ya ce ba da yawun sa suka yi ba.
Kuma bai je har gida ya baiwa malamin hakuri ba, ko ragowar Mutanan da aka ci mutuncinsu. kai ko ta waya ma bai yi ba ballantana mu ce ba da yawun sa suka yi ba.
Muna rokon ALLAH SWT ya raba mu da shugabancin wawaye, don kaunar da muke yi wa ANNABI MUHAMMAD SAW.
Tags
Hausa