Title: SAMARI NE KO YANMATA ? Tare da Fatima Hussain Mohammad.
Salaam, barkan mu da saduwa acikin sabon shirinmu Mai suna samari ne ko yanmata, shiri ne wannan Wanda zai rinka tattaunawa da samari da yanmata Kai tsaye daga Bakunansu,
Akan shin wai tsakanin samari da Yan Mayan su wanene acikin jinsi biyun ke kawo matsala bayan an shafe dogon lokaci ana soyayya babu aure, ko Kuma bayan dogon zango ana soyayya kwatsam sai ace Anrabu da juna?
Wannan Fili namu Kai tsaye zai rinka kawo muku gundarin matsalolin da hanyar magance shi daga bakunan Yan matan mu da samarin, Amma kafin mushifa Kai tsaye cikin Shirin zanso in tofa albarkacin bakina, akan hakan, da DAMA naga budurwa da saurayin da suka shafe shekara da shekaru suna soyayya kamar su hadiye junansu , Wanda zaka ga farkon soyayyar Idan yarinya tana waya da saurayi ko yunwar cikinta bataji, batason Jin Amon kowa inba na karar wayarta ba ,takasa ta tsare tana dakon wayarta tayi kuka.
Da zarar ko ya kira idan tafada daki har mantawa da ita akeyi tana can tana zuba soyayya, haka Shima gogan naka idan yana cikin shaukin Nan na soyayya baya Jin kunyar hirarta agaban kowa baran ma cikin Abokansa, Kai wani ma har cikin gidansu baya iya boye soyayyar shi, a hankali a hankali lokaci na tafiya saiki ga soyayyar naja da baya ko daga wurinshi ko daga wurinta, sannu sannu sai kiganta tafara zama cikin mutane bayan wancan lokacin da ake cikin tsakiyar soyayyar ko yaushe tana cikin dakin kwance kan kujera kamar kyanwa tana Ansa waya.
Shima malamin saika ga Sam ya daina ambaton ta kamar da cikin abokanshi wanima idan aka Anbaceta sai zagi. Shin JAMA a tayaya zamuga an magance irin Hakan acikin Al ummar mu?
Ita Al'adar Mallam bahaushe ko wayasan ba a Jan dogon zangon. ana soyayya batare da iyaye sunshigo Anyi maganar Aure ba, azamanin iyaye da kakanni yaro baya wuce shekara 18 da haihuwa, macce bata wuce 12 ko Sha uku An Aurar dasu ,wallahi idan kaga yarinya takai 15,years saikaji ana yi mata waqa a filin gada bata da saurayi, duk da zamani ne da Allah yakawo mu.
Abinda yasa na shigo da maganar Anawa tunanin ko hangen, adaina daukan dogon Lokaci ana soyayya in har da gaske akeyi kawai Babu zancen zaki jirani sai Nan da shekara uku ko biyu da dai sauran su itama Babu zancen saina gama degree ko makamancin hakan domin kuwa hakan shike kawo yaudara da cin amana wani lokacin ma har wani abunda ba shine ba ya shiga tsakani.....
Tags
Hausa