DR. KABIRU SHINKAFI.MATAWALLE NA BUKATAR GOYON BAYAN ZAMFARAWA

.


Dr. Kabiru Shehu Shinkafi  jigone na jamiyyar APC shugaban kungiyar Asiwaju choice 2023 na kasa kuma tsohon controller na passport a karkashin hukumar immigration ta jahar Oyo.

A wannan hira ta mussamman da mukayi  da shi mun tattauna akan abubuwanda suka shafi rayuwa, siyasa, sha,anin tsaro da dai sauransu.

Kamar yadda yake cewa shi asalin mutumen shinkafi ne a cikin jahar zamfara, ya fito daga gidan Alhaji shehu shinkafi yayi aiki na  immigration na shekaru 35 kafin yayi ritaya bayan ya cika shekarun aikinsa. Dr. Kabiru nada matakin karatu na hudu wato Dr.

SIYASA.

Dr. Kabiru shehu ya shiga siyasa ne bayan ya kammala aikinsa da ya shafe tsawon shekaru talatin da biyar yanayi. Dana tambayeshi banbancinda ya gani tsakanin siyasa da aikin gwamnati yace.

Dr. Kabiru 
"Wato gaskiya akwai banbanci sosai, kasan ni paramilitary nayi kuma lokacinmu akwai da,a da biyayya Wanda yake a yanzu yayi karanci. Sannan akwai rike alkawali.

Sabanin a siyasa inda zakaga gaskiya akwai karanci amana da cika alkawali ba kamar irin siyasar su sardauna ba da mallam Aminu kano da sauransu.

Dukda cewa ba,a taruwa a zama daya, kaga zancen rike alkawalin nan shiyasa naji zuciyata ta kwanta da zabin Sanata Bola Ahmed Tinubu domin mutum ne mai alkawali da taimako. Amma kamarsu Atiku da Obi wa suka taimakawa?

Ai siyasa ba kamar irinta su sir Ahmadu Bello ba. Dukda cewa gaskiya akwai masu rike alkawali da son mutane amma mara alkawalin sunfi yawa. Kaga a zamfara kamar Bello Matawalle, Senator Ahmed Sani Yarima, Senator Kabiru Marafa da Mahmuda Shinkafi mutanen kirki ne kuma suna kokari.


ANN: Kayi magana akan Gwana Bello Matawalle, tsohon gwamna Yarima, Shehi, Senator Kabiru marafa. Shin wace irin shawara zaka bawa shuwagabanin siyasar Zamfara?

Dr. Shinkafi: Shawarata anan gaskiya sai an hada kai, a yaki talauci, a yaki ta,addanci a kuma taimakawa talakawa wudanda wannan mummunan al,amari ya rutsa dasu na barayin daji sannan kuma a kawo masana harkar tsaro su zauna a fidda matsaya ta haryarda za,a magance wannan hali na rashin tsaro.

ANN: kayi magana akan wasu manyan Zamfara inda ka kirasu mutanen kirki masu kaza da kaza shin baka ganin cewa wani zai iya daukar don suna yan jam,iyyarku ne kake yabonsu haka?

Dr. Kabiru: Sam ba haka bane, wudannan mutanen dana ambata Sam babu Wanda ya sanni ma a cikinsu na gaya ma na dade ina aiki a jahohin kudancin kasar nan kusan duk rayuwar aikina daga Lagos, sai Oyo, sai Port Harcourt. Amma a matsayi na na babban Jami,in tsaro ai inada rahotanni da boye dana fili, ina alaka da mutane kuma ina zuwa gida bayan haka ina karance karance. 

Yanzu misali ka dauki sanata Sahabi Ya,u Kaura sanata mai wakilta ta a majalisa, ai shima dan jamiyyata ne, me yasa ban yabeshi ba?  Bari in gaya ma naje gidanshi Abuja waiga dan uwa mu gaisa in dan bada shawarwari a matsayina na tsohon Jami,in tsaro to wallahi dani da direbana da PA ne ko ruwa ba,a bamuba haka ake siyasa?

 Ni ban taba jin Wanda akace wai sahabi ya,u ya taimakawa ba. Ba wai naje neman kudi wajenshi ba tunda alhamdullahi inada nawa rufin asiri daidai gwargwado.

Amma kaga wanban shinkafi shima mutum ne ne mai kirki da son mutane naje gidanshi ya yayi man taro na mutumci kuma munyi maganganu masu muhimmanci, irin wudannan mutanen ne ya kamata su samu mulki ko a basu mukami domin zasu taimakawa al,umma. 

ANN : A matsayinka na Jami,in tsaro wace irin hanya kake gani ya dace gwamnatin Zamfara ta bi domin tabbatarda tsaro a jahar? Kuma wane irin kira zaka yiwa yan jahar da suke cikin mawuyacin hali?

Dr. Kabiru: Gaskiya sai an zauna anyi gyara, sai an shigo da masana harkar tsaro da masana rayuwar dan Adam, gwamna Bello Matawalle na matukar kokari kuma yana bukatar addu,a da goyon bayan zamfarawa domin samun ingantaccen tsaro. Bayan haka ya kamata a bullo da hanyoyin taimakawa talakawa domin rage radadin ta,addanci. Muna kuma bukatar wutar lantarki da sauran kayan more rayuwa da zasu taimaka wajen rage zafin talauci, anan ma in sha Allahu idan sanata Tinubu ya zama shugaban kasa tabbas zai taimakawa zamfara wajen gina kasa, samarda aikinyi ya kuma yi maganin rashin tsaro.

ANN: 
Shin kana ganin jamiyyar APC zata iya lashe zaben shekarar 2023 duba da irin sha,anin tsaro?

Dr. Kabiru: Tabbas kuwa ai zamfara jahar APC ce, kuma duk dan zamfara yasan jam,iyyar PDP ita ta samu cikin halinda muke, domin a lokacinsu ne matsalar tsaro ta fara. Kuma da sukaje gyara sai suka kashe maciji basu sare kan ba.
Ina maka aljawarin cewa idan sanata Tinubu ya hau mulki in sha Allahu zamu fito da tsare tsare wudanda zasu magance tsaro su kuma rage zafin radadin ta,addanci a jahar zamfara. 


ANN. To Dr Kabiru muna godiya da lokacinka kuma in sha Allahu zamu ringa tuntubarka daga lokaci zuwa lokaci domin jin ta bakinka a kan muhimman abubuwa.

Dr. Kabiru : Nima na gode.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post