A cikin tattaunawar da manyan ƴan jaridar Nigeria suka yi da shugaba Buhari, sun taɓo matsalar tsaron Nijeriya, inda suka kawo masa ƙorafi da zargin cewa; akwai sa hannun jami'an tsaron Nijeriya a cikin taɓarɓarewar tsaron nijeriyar! Da masaniyar su akan duk duk wani ta'addanci dake faruwa a cikin ƙasar nan!
To anan ne shugaba Buhari ya ce; lallai kam Biri ya yi kama da mutum! Domin tun da ya hau kujerar shugabancin ƙasar nan sau ɗaya kawai ya taɓa canja su!
Shugaba Buhari ya ce; wasu daga cikin su, su jami'an tsaron najeriyar sun yi shekara sha biyar (fifteen years) zuwa shekara ashirin (twenty years) suna aikin! Ya kamata a ce sun gano lalatattun cikin su masu kawo masu tarnaƙi a cikin aikin tabbatar da tsaron ƙasar nan! Ya kuma ce idan har suka yi sakaci suka bari al'amurra suka dagule, to sune zasu fara kuka da kan su! Domin babu wanda zai je ya tura tsohon soja akan aikin tabbatar da tsaron ƙasa, su dai ne dake cikin aikin za'a tura!
To jami'an tsaron mu kun dai ji, da fatan zaku miƙe tsaye ku yi iya ƙoƙarin ku domin ku ga an sami ingantaccen tsaro a cikin ƙasar nan! Kuma da fatan zaku tashi tsaye sosai domin ku yaƙi gurɓatattu daga cikin ku masu yiwa ƴan ta'adda aiki! Kuma kun sani cewa; duk abinda kuke bukata na kayan aiki ko kuɗi, gwamnatin Nijeriya tana baku! To me kuke nema kuma?!
Allah Ya kyauta kuma Ya Kawo mana ƙarshen maciya amanar tsaron ƙasar nan!
Ameen!