Rubutawa: Mohammed Bello Doka
A wata ganawa da manema labarai ta sati sati da jakadan kasar Falasdin a Najeriya Abdallah M. Abu Shawesh keyi, jakadan yayi Allah wadai da irin kisan kiyashin da kasar Israila Keyi a zirin Gaza.
Mr. Abdallah yace ranar 15, ga watan mayu ranace ta tunawa da Kisan Kiyashin da Falasdinawa kewa lakabi da Nakba, Yana mai cewa a shekarar 1947 zuwa 1948, kasar ta Israila hadi da goyon bayan kasar Amurka da Burtaniya suka gudanarda kisan kare dangi da yayi sanadiyar mutuwar dubban Falasdinawa aka kuma jikkata kusan Falasdinawa milyan daya tareda kore su daga wajajen zaman su aka kuma raba kasar ta Falasdin gida uku aka bawa yahudawa kashi biyu su Kuma Falasdinawa aka bar masu kashi daya.
Abdallah ya kara da cewa a yayin wannan Nakba kasar ta Israila ta kashe Falasdinawa kimanin 15,000 ta kuma jikkata tareda tarwatsa kimanin Falasdinawa 950,000 wudanda suka zamo yan gudun hijira. Haka Kuma a wannan lokacin Israila ta tarwatsa garuruwan Falasdinawa 1,300.
Kawo yanzu a wani sabon yunkurin kawarda kasar ta Falasdin daga bayan kasa, a wani yaki da Israila ta fara ranar 8 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata kasar ta Israila ta kashe kimanin Falasdinawa 45,091 a ciki akwai mata 15, 103 da kananan yara 9,961, yan jarida 142 da kuma maaikatan lafiya 492. Kimanin mutane 10,000 ne suka bata a lokacinda mutum 78,404 suka jikkata. Mr. Abdallah ya kara da cewa yanzu haka kimanin yara marayu 17,000 ke rayuwa a Falasdin ba tareda iyayen su ba sanadiyar wannan aika aikar.
Mr. Abdallah yayi kira ga kasashen duniya dasu matsa su kuma kara kaimi wajen tabbatarda an kawo karshen wannan kisan kiyashin da kasar ta Israila ke aikatawa tare da goyon bayan kasashen turai musamman kasar Amurka.
Masu ruwa da tsaki daga sassa dabban dabban na duniya na zargin kasar Amurka da hannu dumu dumu wajen aikata wannan kisan kiyashin da kasar Israila keyi a zirin Gaza, duba da cewa kimanin kashi 85% cikin dari na makaman da kasar Israila ke amfani da su kirar Amurka ce, haka kuma kudade da sauran fasahohin yaki da Israila ke amfani da su duk sun fito ne daga kasar ta Amurka.
A dayan bangaren Kuma gwamnatin Amurka a karkashin jagorancin shugaba Joe Biden na barazana ga babbar kotun hukunta laifukan yaki ta ICC dake birnin Hague domin yunkurin da kotun keyi na bada dokar kama Firaministan kasar Israila Benjamin Netanyahu akan laifukan yaki.
An dai shafe watanni ana wannan Shari,ar a babbar kotun ta duniya inda kasar Afrika ta Kudu ta shigarda kasar Israila akan aikata laifukan yaki a zirin Gaza.
Kasashe da dama kamar su Ireland, Brazil, China, Russia da sauransu sun goyi bayan kotun ta ayyana kasar Israila akan aikata laifukan yaki, ta kuma bada damar kama shuwagabannin Israilan akan laifukan yaki, kisan kare dangi da kuma kisan kiyashi.
Mafi yawancin kasashen duniya sunyi amanna da wannan kiran, amma kasar ta Amurka ta buga kai da kasa tace sam bata aminta ba, har tana barazana kakabawa kotun takunkumi, da kuma alwashin hukunta alkalan kotun idan suka sake suka caji kasar ta Israila da laifukan yaki.