Shin Ana Cire Sarki A Kuma Dawo Da Shi Ya Cigaba Da Sarauta?

Mohammed Bello Doka

Ko Kun San Ana Cire Sarki A Kuma Dawo Da Shi Ya Cigaba Da Sarauta?

A daidai lokacinda ake ta rade radin cewa sabon Gwamnan Kano na makarkashiyar tuge Sarkin Kano mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero daga sarautarsa domin dawowa da aminin mai gidansa Mai martaba Sanusi Lamido Sanusi wanda tsohuwar Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta tsige, masana masu bincike kan sarautar gargajiya da al,adu sunyo mana wannan binciken. 

A wani takaitaccen bayani dake yawo a yanar Gizo masanan da ba,a san ko su wayeba sun fito da jerin sunayen wasu Sarakuna da suke ikirarin an ciresu daga sarauta kuma sundawo. 

Shin wannan abu ne mai yiyuwa a Kano, ko a,a.    Wannan abune da Allah ya barwa kanshi sani domin shike bada mulki kuma shine mai karbewa

Ga Jerin Wasu Sarakunan Kasar Hausa da Aka Cire Kuma Aka Maido Su Kan Karagar Mulki

1-Sarkin Kano Muhammadu Kukuna (1651-1652), ya dawo (1652-1660)

2-Sarkin Zazzau Abdullahi Dan Hammada (1851-1871), ya dawo (1874-1879)

3-Sultan Na Damagram Abubakar Sanda (1978-2000), ya dawo (2011-date)

4- Sarkin Sudan Na kwantagora Ibrahim Nagwamatse (1880-1904), ya dawo (1906-1929)

5-Sarkin Zazzau Suleja Muhammad Auwwa Ibrahim (1993-1994), ya dawo (2000-date)

6-Sarkin Hadejiya Buhari (1848-1850), ya dawo (1851-1863)

7-Sarkin Daura Tafida dan Lukudi (1877-1884), ya dawo (1891-1904)

8-  Sarki Agaie Muhammad Nkochi Attahiru (1989-1994), ya dawo (2001-2004)

9-Shehun Borno Umar Ibn Abubakar Garbai (1903-1905), ya dawo (1906-1917)

10- Sarkin Jama’a Abd ar-Rahman (1837 - 1846) ya dawo ( 1849 - 1850)

11- Sarkin Jama’a Musa dan `Usman (1846 - 1849) ya dawo (1850 - 1869)
12- Sarkin Jama’a Adamu Usman (1869 - 1881) ya dawo (1885 - 1888)

13- Muhammadu Adda

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post