Edo 2024 Dr. Mary Alile Mikiya Mai Hangen Nesa.

A daidai lokacinda zaben Gwamnan jahar Edo da za,a gabatar shekara mai zuwa ke kara matsowa CAPACITY MEDIA tayi ninkaya tare da nutso domin hango irin gudunmawarda shugabar matan jam,iyyar APC Dr. Mary Alile ke bayarwa domin cimma Nasara akan wannan muhimmin zabe mai zimmar kwato jahar daga halin waini yasu data samu kanta a ciki. 

Kamar yadda rahotanni suka gabata Dr. Mary Alile ta shafe kwanaki ana bincike kafin ta gwangwaje mataimaka na musamman guda 18 a jahohin Ondo da Edo. Tunidai ragotanni sun nuna cewa wudannan mataimaka na musamman sun dukufa wajen yada manufar jam,iyya a wudannan jahohin.

Haka kuma shugabar matan tare da mataimakan nata sun dukufa wajen yada manufar sabunta zato ta gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Haka kuma CAPACITY MEDIA ta kara bankado wni yunkuri inda shugabar matan ta hada duk kungiyoyin mata masu zaman Kansu dakeda register a ofishin shugabar matan a katkashen tuta daya domin samarda matsaya da kuma hada karfi da karfe wajen cimma nasara a wudannan jahohin na Edo da Ondo. 

Cikin watanni hudu da kama aiki shugabar matan ta nuna kwarewa da hazaka da kuma manufar aiki tukuru domin cimma nasara a jam,iyyance da gwamnatance. 

📷 *CAPACITY MEDIA HAUSA*

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post