Kungiyar nan mai fafutukar tallafawa mata da kananan yara ta Sister-to-Sister Worldwide a karkashin jagorancin shugabar mata ta jam,iyyar APC ta kasa Dr. Mrs. Mary Alile tayi bikin cika shekaru bakwai da kafuwa.
Wannan gagarumin bikin da akayi a ranar 14 ga watan nuwamban 2023 a birnin Benin na jahar Edo ya samu halattar manyan yankasuwa, jami,an gwamnati da masu ruwa da tsaki daga sassa dabban dabban.
Rassa da cibiyoyin kungiyar daga jahohi dabban dabban sun hallaci wannan taron domin taya Dr. Mrs. Mary Alile murnar wannan gagarumar nasara.
Haka ma muhimman mutane kamarsu Maj. Gen. Charles Orhiavbere, babban bakon bikin, Amb. Sunday Osemwigie (Boston) da kuma unban kungiya Chief Bar. Bisi Idaomi sun bada muhimmiyar gudun mawa a wannan taron, tare kuma da shan alwashin ci gaba da taimakawa Dr. Mrs. Mary Alile domin ganin ta cimma manufarta wajen kaiwa talaka dauki.
A lokacinda take nata jawabin shugaban kungiyar kuma shugaban matan Jam,iyyar APC ta kasa, Dr. Mrs Mary Alile tayi godiya ga dukkan wudanda suka samu damar halattar taron, dama wudanda basu hallaci taron ba dake wa kungiyar fatan alkhairi.
Ta kara da cewa ta kafa wannan kungiyar ne shekaru 7 da suka gabata da zimmar tallafawa mata da kananan yara a sassa dabban dabban na rayuwa, ta kuma yi nuni da cewa kungiyar ta samu nasarori mabanbanta kawo yanzu.
A wannan taron na bana kuma an samu nasarar kafa wata gidauniya da zata tallafawa mata masu jego da matsuguni suda yayansu domin rage masu radadin talauci da halin kakanikayi.
A nata jawabin shugabar zantarwa kungiyar wato National Coordinator a turance Mrs. Racheal Edoba tayi godiya ta mussamman ga bakinda suka samu halattar taron, ta kumayi adduar Allah ya maida kowa gida lafiya.
Taron ya rufe da fatan alkhairi da kuma kade kade da wakewake daga yan kungiyar dama wasu masu mata fatan alkhairi.
CAPACITY MEDIA HAUSA