Hajiya Mansurah Jimoh ta Mika Godiya ta Musamman ga Dr. Mrs. Mary Alile

Shugabar kungiyar "No Woman No Nation" ta kasa Hajiya Mansura Jimoh ta mika godiya ta musamman ga Shugabar Matan jam,iyyar APC Dr. Mrs. Mary Alile.

Ta kara da cewa jajircewar Dr. Mary wajen tallafawa mata da kuma basu damar fadan albarkacin bakinsu a cikin jam,iyyar mai mulki abun a yaba ne. 

Ta kumayi yaba kwazo da kokarin Dr. Mary wajen tallafawa da kuma bawa mata damar suma su fito a dama dasu a siyasa. Tace wannan gagarumar nasara ce ga jam,iyyar ta APC. 

Tabbas wannan yunkurin naki zai taimaka wajen kawo cigaban jam,iyyar, dama kasa baki daya inji Hajiya Mansurah.

Ta kara da mika godiya da kuma fatan alkhairi ga Dr. Mary Alile tare kuma da yin adduar Allah ya baiwa Dr. Mary karfi da kwarin guiwar ci gaba da wannan abun a yaba. 


Daga karshe tayi kira ga ilahirin mata na ciki da wajen jam,iyyar ta APC dasu bawa Dr. Mary Alile goyon baya wajen sauke wannan nauyi. 

CAPACITY MEDIA HAUSA.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post