Shugaban Matan Jamiyar APC Dr. Mrs. Mary Alile Damana Gidan Albarka

Ko shakka babu babar Jami,yya mai mulki ta APC  tayi tunani mai zurfi a matakinda ta dauka na nada Dr. Mrs. Mary Alile a matsayin shugaban matan jam,iyyar ta kasa a ranar 25 ga watan Ogustan shekarar bana ta 2023.

Dr. Mary ta nuna kanta a matsayin mikiya mai hangen nesa, kuma damina uwar Albarka, domin kuwa tun daga rana ta farko da aka nada ta a wannan matsayin take aiki tukuru, tare kuma da amfani da kungiyarta mai suna " "Sister- To- Sister World Wide" wato " daga Yar uwa zuwa Yar Uwa a duk fadin duniya" a Hausance domin taimakawa al, umma a gida  Najeriya da kuma  sauran kasashen duniya. 

Wannan kungiyar an kirkiretane domin taimakawa mata a duk fadin duniya a fanni dabban dabban da suka shafi yaki da talauci, taimakawa wajen bawa yaya mata ilimin zamani, kula da lafiyar mata, gajiyayyu hadi da ilmantarwa da tufatarwa da kuma taimakawa mata akan harkokinda suka shafi kiyon lafiya, samun sana,a da kuma bada hannun jari. Tabbas wannan dalilin ne yasa Dr. Mrs. Mary Alile tayi fice tare kuma da jan dandazon al,umma a duk inda ta bayyana. 

Tabbas Dr. Mary ta nuna kwarewarta, bawai kawai wajen bada taimakon kudi ko kayan masarufi ba, a, a harda ma wajen bada shawarwari, jawo hankalin mata da kananan yara akan hanyoyin na gari, bada kulawa ta musamman ga gajiyayyu da sauransu. 

Tabbas zamanta shugaban mata na jammiyyar APC ta taka muhimmiyar rawa wajen hada kan matan Jami,iyyar a duk fadin kasar. 

A wani yunkuri na musamman da ba,a taba ganin irinsa ba a jam,iyyar mai mulki Dr. Mrs. Mary ta nada masu taimakawa na musamman akan gangami a jahohin Edo da Ondo domin taimakawa wajen yada manufa da gangamin al,umma a yakin neman zaben shekara mai zuwa 2024. 

Tabbas Dr. Mrs. Mary Alile tayi fice ta kuma cancanta a kudurin sabunta zato na gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.  A matsayin mu na yan kasa babu abunda zamuce sai fata na alkhairi.

📷 Capacity Media.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post