Alile Coalition Initiative, ina mai mika sakon taya murna ga shugabar kungiyar Sister-to-Sister Worldwide Dr. Mary Alile dama yan kungiyar baki daya akan bikin cika shekaru 7 da kafuwar kungiyar.
Ina kuma tayaki murna akan kafa gidauniyar samarda matsuguni ga mata masu juna biyu a karkashin kungiyar taki, tabbas wannan yana nuni ne ga irin tausayi, jinkai da kuma tattausar zuciyarki akan marasa galihu, wannan abun a yaba ne.
Ina maki fatan alkhairi ina kuma yi maki addu,ar samun nasara, tareda goyon bayan masu hannu da shuni da kuma masu rike da madafun iko, domin tallafa maki wajen cimma wannan buri da kuma ci gaba da Bayarda tallafi da jinkai kamar yadda kika saba shekaru aru aru.
Ina kuma mai yi maki albishir da cewa zan kasance mai bada goyon baya dari bisa dari domin cikar wannan buri naki.
Daga karshe Ina maki adduar karin lafiya da nisan kwana da kuma karfin ci gaba da tallafawa bil,Adama a duk fadin duniya.
Sa hannu:
Hon. Pius Alile
Shugaban kungiyar Pius Alile Coalition Initiative, PACI