Dr. Mrs. Mary Alile tayi Kira akan Kawo Karshen cin Zarafin Mata

Yau, 28 ga watan Nuwamba, 2023, shine kwana na hudu a cikin jerin gwanon kwanaki 16 da majalisar dinkin duniya ta ware domin yaki da cin zarafin mata a duk fadin duniya. 

Shugabar kungiyar "Sister to Sister Worldwide " kuma shugabar matan jam,iyyar APC ta kasa wato Dr. Mrs. Mary Alile tayi kira ga masu ruwa da tsaki da zimmar dakile wannan mummnunar al,adar ta cin zarafin mata. Tace kudurin tabbatarda adalci ga mata ne ya bata karfin guiwar kafa kungiyar ta Sister to Sister Worldwide wacce a yanzu takeda rassa a Nahiyoyi hudu na duniya da kuma kasashe 9 a fadin duniyar. 

Tayi wannan jawabin ne a wata hira ta musamman da manema labarai a birnin Benin na jahar Edo kwanaki kadan bayan bikin cika shekaru 7 da kafuwar kungiyar ta Sister to Sister Worldwide da ya gudana a birnin na Edo. 

Ta kara da cewa magance cin zarafin mata na bukatar ilmantarwa, fadakarwa da kuma wayar da kan al,umma dasu fahimci cewa wannan ba abu bane mai alfanu da zai haifawa al,umma da mai ido ba. 

Dr. Mary batayi kasa a guiwa ba inda ta dauki lokaci tana bayani akan irin kalubalenda ta fuskanta a matsayinta na ya mace tun tana karama har I zuwa yau. 

Ta kumayi kira ga masu ruwa da tsaki akan hada karfi da karfe wajen tallafawa mata domin su samu damar fuskantar matsalolinda sukayi katutu a cikin al,umma a wannan lokacin. 

CAPACITY MEDIA HAUSA.

Post a Comment

Share your thoughts with ANN..

Previous Post Next Post