Masu iya magana sukace lafiya jarice, a bisa wannan manufar ce gwamnan Kogi Alhaji Yahaya Bello Ya gwangwaje birni da kauyukan Kogi da asibitocin Zamani na azo a gani.
Tabbas kokarin gwamnan a fanni kula da lafiya ya cancanci yabo. Haka ma yunkurinda yakeyi wajen farfadowa da kuma bada ingantaccen ilimi ga yanjahar, gina tituna da sauran ababen more rayuwa ya zamo abun yabo tare kuma da zama izna ga yan adawa.
A cikin wannan satin ne jama,ar Kogi me cike da tsammani da kuma zato na gari domin wannan satin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sauka jahar wajen qaddamarwa da kuma bude ayukka dabban dabban na more rayuwa da hazikin gwamnan ya gudanar a jahar.
Kadan daga cikin ayukkan sun hada da Asibitoci na zamana a bangarori mabanbanta na jahar, sai sadoji, tituna da kuma hanyoyin sufuri domin inganta rayuwar yan jaha dama yan kasa baki daya.
Babu shakka tarihi bazai taba mantawa ba da irin wannan qwazo na hazikin Gwamna a jahar.
Tags
Hausa