Kamar yadda ma,abota shafukan sada zumunta keta yawo da hotuna da bidiyoyi na ayukka dabban dabban na gina kasa da mai girma gwamnan Kogi Alhaji Yahaya Bello Keyi bincikenmu na yau ya garzaya ne zuwa wajaje guda biyu.
Waje na farko shine babbar asibitin zamani ta karamar hukumar Gegu wadda an riga da an kammalata, a wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zamunta za,a iya ganin gwamnan tareda dinbin mabiya,ma,aikata da masu goyon bayansa suna zagaya asibitin inda masu kallo ke san barka.
A bidiyon mai tsowon minti daya da yan dakikai za,a iya ganin sassa dabban dabban na asibitin cike da kayan aiki na zamani, dakunan jinya, dama dakunan shan magani duk cike da kayan aiki na zamani da inganci.
A dayan bangaren kuma wani katafaren gini ne na sabuwar asibitin Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta Wanda aka kusan kammalawa.
Kamar dai a Gegu shima wannan ginin yana dauke da dakunan jinya, dakunan shan magani da dakuna dabban dabban cike da kayan aiki na zamani. Domin masu iya magana kance lafiya jarice kuma kula da lafiya na mai ilimi ne.
Wannan ya janyo ceccekuce a kafafen sada zumunta inda al,umma daga sassa dabban dabban na jahar dama kasa baki daya keta godiya da sambarka da irin wudannan ayyuka na alkhairi da gwamnan keyi a birni da kewayen jahar ta Kogi. Tare da kuma ci gaba da masa adduoin nasara da ci gaba.
Tags
Hausa